✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mai ciki da wasu 3 a Anambra

Maharan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu ciki har da wata mai juna biyu a yankin Eziani na Karamar Hukumar Ihiala a Jihar Anambra.

Rahotanni sun ce an kai harin ne da misalin karfe 1 na daren ranar Talata.

“Bincikenmu ya gano cewa maharan sun yi amfani da harsashin bindiga AK-47 wajen kashe mutum hudu wanda ba su ba su gani b,” in ji Tochukwu Ikenga, kakakin ’yan sandan jihar.

’Yan bindigar sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi ajalin mutum hudu nan take.

Kakakin rundunar ya ce an mika gawarwarkin mutanen da aka kashe zuwa dakin ajiye gawa don gudanar da bincike.

Jihar Anambra kamar wasu daga cikin jihohin Kudancin Najeriya na fuskantar hare-haren ’yan bindiga, ba dare ba rana.