✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe malami a makarantar sakandaren jihar Nasarawa

Sai dai 'yan sanda sun ce 'yan fashi ne ba 'yan bindiga ba

Wasu ‘yan bindiga sun harbe wani malami mai suna Auta Nasela har lahira, a Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Kimiyya da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon ta Nassarawa.

Lamarin dai ya faru ne ranar Asabar da karfe 8:45 na dare, lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari makarantar, suka kuma shiga gidan malamin tare da bukatar ya ba su kudi.

Aminiya dai ta gano yadda firgici ya sanya malamin kokarin tserewa gidan makwabcinsa, wanda ya sanya ‘yan Bindigar suka bude masa wuta.

Wani malami mai suna Mista Timothy Malle, shi ma ya sami raunuka yayin da ‘yan bindiga ke harbin Auta, kuma yanzu haka ya na asibiti a kwance yana karbar magani.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ba na garkuwa ba ne, ya fi kama da fashi da makami.

Ya kuma ce sun samu kiran gaggawa daga karamar Hukumar cewa ‘yan daba ne suka aikata ta’asar.

Ya kuma ce zuwansu ke da wuya suka gaggauta mika shi asibiti, kasancewar ‘yan bindigar sun tsere, shi kuma malamin daga baya ya ce ga garinku nan.

Kakakin ya kuma ce Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya ba da umarnin bincike kan lamarin domin kamo wadanda suka aikata laifin don su girbe abin da suka shuka.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Yuli ne Gwamna jihar, Abullahi Sule ya ba da umarnin rufe makarantun firamare da na sakandare a jihar, biyo bayan barazanar tsaro da ya ce ta mamaye Birnin Tarayya da ke da makwabtaka da jihar.