✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe mutane da dama a kasuwar Sakkwato

Harin ya yi sanadiyyar kashe ’yan kasuwa da masu sayayya da masa a kasuwar.

Mutane da dama  ne aka kashe yayin wani hari da ’yan bindiga suka kai wata kasuwa da ke Gabashin Jihar Sakkwato ranar Lahadi.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun yi dirar mikiya ne a kasuwar mako-mako ta Karamar Hukumar Goronyo da ke Jihar.

Lamarin dai ya yi sanadiyyar kashe ’yan kasuwa da masu sayayya da masa a kasuwar.

Har yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma wakilin Aminiya ya gano cewa maharan sun shafe sa’o’i da dama suna cin karensu ba babbaka ba tare da an kai wa ’yan kasuwar dauki ba.