✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 11, sun yi garkuwa da 7 a Sakkwato

An kai hare-haren ne cikin kwana biyu a kauyuka biyar

Yan bindiga dauke da manyan makamai a kan babura fiye da 200 sun kashe mutum 11 tare da sace wasu bakwai a kauyuka biyar na Karamar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun kai hari kan kauyukan ne a cikin kwana biyu.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa hare-haren sun jefa su cikin damuwa da tashin hankali.

A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, “’Yan bindiga sun matsa mana, suna cin karensu ba babbaka kuma Gwamnatocin Najeriya sun kyale mu ana yi mana wulakanci babu dauki ko kadan.

“A jiya [Lahadi] ’yan bindigar nan da yawansu sun shiga cikin garin Kurawa sun kashe mutum biyu, suka dawo Gumozo suka kashe uku, suka tafi Jijjira bayan ba-ta-kashi da su da mutanen gari suka kashe mutum daya.

“A ranar Litinin kuma sun dawo a kan babura sama da 200 suka tafi kauyen Dan Garin Mutum suka kashe mutum biyar, a Gatawa mutum biyu bayan da aka yi dauki-ba-dadi tsakaninsu da mutanen gari da taimakon wasu sojoji aka kora su wajen gari,” a cewar majiyar.

Hari ila yau, majiyar ta ce ba a san adadin mutanen da ke hannun ’yan bindigar ba.

Sai dai a cewar majiyar, an sami nasarar an kubutar da mutum bakwai da suka yi garkuwa da su a garin Dan Marke, bayan an biya fansar Naira dubu 100 kan duk mutum daya.

“Muna cikin wahalar mutanen nan a ranar Litinin da ta gabata sai da suka tare hanyar Sakkwato zuwa Sabon Birni sau tara, hakan ya sa ba wata motar da ta shigo nan ko ta fita, a kullum kuwa akalla sai an samu mota 20 da za su yi lodi zuwa Sakkwato, a yanzu kayan masarufi sun fara yanke mana, ka ajiye maganar abinci domin duk wanda ya yi noman rani suna sanya shanunsu suna cinyewa tun daga Gangara abin ya kusa shigowa Sabon Birni,” in ji shi.

Dan Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar mazabar Sabon Birni,  Aminu Almustafa da aka sani da Boza ya tabbatar da hare-haren da kuma sace mutanen.

Ya ce, “A wata daya, an kashe mana mutum sama da 20 ba wani mataki da muka ga an dauka game da magance mana matsalar da muke ciki, muna ta magana an kyale mu da manema labarai muna fadin halin da muke ciki amma ba wani matakin a zo a gani,” a cewarsa.

Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin tabakin jam’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Sanusi Abubakar, ya ci tura domin wayar shi ba ta zuwa har lokacin hada wannan rahoton.