✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 45 a Zamfara

Mata da kananan yara sun fantsama cikin daji babu wanda ya san halin da suke ciki.

Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa, ’yan bindiga sun kashe akalla mutum 45 yayin hare-haren da suka kai wasu kauyuka shida na Jihar a ranar Laraba.

Gomman mutane da ciki har da mata da kananan yara sun fantsama yayin da maharan suka kona gidaje da shaguna da wasu gine-ginen al’umma.

Aminiya ta ruwaito cewa, an kai harin ne a Yankin Magami da ke Karamar Hukumar Gusau wanda ya shafi garuruwan ’Yar Doka, Kango, Ruwan Dawa, Madaba, Arzikin Da da kuma Marairai.

Mazauna sun shaida wa Aminiya cewar ’yan bindigar sun fara kai harin ne a kauyen ’Yar Doka da ke da tazarar kilomita bakwai tsakaninsa da garin Magami haye a kan Babura inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Wani da ya tsira, Halliru Bala, ya ce mutane da dama sun fantsama cikin daji domin neman tsira da rayukansa, sai dai “babu wanda ya san halin da suke ciki a yanzu.”

Halliru ya ce bayan ’yan bindigar sun kammala cin karensu babu babbaka a kauyen ’Yar Doka kuma suka nufaci kauyen Kango inda suka harbe mutum 11.

Ya ce sun kuma kashe mutum 13 a kauyen Ruwan Dawa da ke kan hanyar Gusau zuwa Dansadau mai tazarar kilomita tsakaninsa da garin Gusau, babban birnin Jihar.

“Sun kuma harbe mutum bakwai a Madaba, biyu a Marairai da kuma wasu biyar a Arzikin Da.

“A yanzu da nake magana da ku, an kawo gawarwakin mutum bakwai garin Magami, inda za a yi musu jana’iza da zarar an kammala buda baki,” inji Halliru.

Halliru ya ce galibin wanda aka kashe mutane ne da suka fita kai dauki kauyukan da suka samu labarin ’yan bindigar sun kai musu hari.

Kazalika, wani mazauni mai suna Babagida, ya ce, “’yan bindigar da suka kai musu hari sun kone musu rumbunansu na abinci, lamarin da ya sanya suka nemi mafaka a garin Magami.”

Yayin da aka nemi jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya bukaci a bashi lokaci domin tabbatar da aukuwar lamarin.

Sai dai Kwamishinan yada labarai na Jihar, Ibrahim Dosara, bai ce komai a kan lamarin ba, inda ya yi Allah wadai da harin da aka kai ranar Talata a garuruwan Gobirawa, Gora, Rini da Madoti Dankule da ke Karamar Hukumar Maradun.