✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum biyu a Kaduna

’Yan bindiga sun harbe wasu matasa a yankin Juji da ke Karamar Hukumar Chikun ta Kaduna. Maharan sun yi danyen aikin ne ran Alhamis inda…

’Yan bindiga sun harbe wasu matasa a yankin Juji da ke Karamar Hukumar Chikun ta Kaduna.

Maharan sun yi danyen aikin ne ran Alhamis inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.

Wakilinmu ya fahimci cewa mutum biyun da ’yan bindigar suka kashe sun kai dauki ne daga unguwar Babbar Saura da ke makwataba da juji bayan sun ji karar harbi.

Shugaban matasan unguwar Juri, Kwamaret Hosea Bawa da ’yan kwamitin tsaro na sa kai sun tabbatar da faruwar lamarin da mutuwar matasan.

“Maharan sun shigo unguwarmu jiya (Alhamis) da misalign 11.00 na dare. Mun yi dauki ba dadi da su amma sun kashe matasa biyu ’yan Babbar Saura da suka kawo mana dauki”, inji Hosae.

Sai dai ya ce babu wanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da shi a unguwar da karuwar hare-hare ya sa mazauna kafa kwamitin tsaro na sa kai da ke yin sintiri.

Zuwa lokacin hada wannan rahoto Kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, Mohammed Jagile bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ba.