✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum uku a Kaduna

Da Yammacin ranar Talata ne wasu ’yan bindiga suka kai sabon hari kauyen Ganji da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, inda suka kashe…

Da Yammacin ranar Talata ne wasu ’yan bindiga suka kai sabon hari kauyen Ganji da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum uku yayin da kuma wasu akalla biyar suka tsira da raunuka na harsashin bindiga.

Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa, ’yan bindigar sun far wa kauyen Ganji mai makwabtaka da na Albasu, wanda a bara suka kai wa hari a kan baburwa inda suka kona gidaje da wata mota.

Wani mazaunin kauyen mai suna Lado Ibrahim, ya ce maharani sun yi wa garin shigar bazata ne da misalin karfe biyar na Yamma haye a kan Babura fiye da talatin da mutum biyu a kan kowannensu.

Ya ce isowar ’yan bindigar ke da wuya suka shiga harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da tuni aka garzaya da mutum biyar zuwa

Kazalika, ya ce a halin yanzu a garzaya da mutum biyar zuwa asibiti inda suke ci gaba da jinya sakamakon rauni na harsashin bindiga da suka samu kuma jirgin sojoji mai saukar angulu na ci gaba da shawagi domin fattatakar maharan daga kewayen kauyen

Wani mazaunin kauyan mai suna Hamza Shafiu, ya ce akwai yiwuwar wannan sabon hari na da nasaba da makamancinsa da ’yan bindiga suka kai a ranar Litinin wanda suka yi awon gaba da mutane.

Yunkurin da wakilin Aminiya ya yi na neman jin ta bakin Kakakin rundunar ’yan sandan jihar ASP Muhammad Jalige, ya ci tura a yayin da bai amsa kiran wayarsa ba da kuma sakon kar ta kwana da aka aike masa.