✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 7 a Zamfara

’Yan bindigar sun yi wa ’yan sandan kwanton bauna a Kauyen Zonai da ke garin Magami.

Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun kashe akalla ’yan sanda bakwai da suka yi wa kwanton bauna a kusa da Kauyen Zonai da ke Gundumar Magami ta Karamar Hukumar Gusau a Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun bude wa motar ’yan sandan wuta ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga bakin aiki a wani shingen binciken ababen hawa da suka kafa a Kauyen Zonai da ke kan hanyar da ta ratsa cikin Magami daga Gusau zuwa Dansadau.

“Wannan lamari abun bakin ciki ne musamman a gare mu mutanen Magami saboda yadda ’yan sandan suka taimaka gaya wajen magance aukuwar munanan ababe na rashin tsaro a wannan hanya.

“Hakika, kasancewarsu a wannan shingen binciken ya bai wa matafiya kwarin gwiwa na bin hanyar.

“Babu shakka an sace tare da kashe gomman mutane a kan hanyar mai nisan kilomita 50 daga Gusau zuwa Magami.

“Wannan ba karamin abin takaici bane a gare mu”, inji wani mazaunin yankin mai suna Halliru.

Neman jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu bai yi nasara ba a yayin hada wannan rahoto.

Sai dai Jami’in Hulda da Alumma na Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau, Awwal Usman Ruwandoruwa, ya shaida wa Aminiya cewa an kawo musu gawawwakin ’yan sandan da misalin karfe 8.00 na safiyar Talata.

A watan Yulin da ya gabata ne wasu ’yan bindiga suka kashe ’yan sanda 13 a kusa da Kauyen Kurar Mota da ke kan hanyar da ta ratsa Dankurmi daga Magami zuwa Dangulbi.