✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun koma amfani da wayoyin ‘oba-oba’

An kama ’yan bindiga 724 a cikin wata takwas, 296 na fuskantar shari'a

Gwamnatin Katsina ta ce ’yan bindigar jihar sun koma amfani da wayoyin sadarwa na ‘oba-oba,’ bayan katse hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 13 na jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce duk da cewa matakan da gwamnatin jihar ta dauka na dakile ayyukan ’yan bindigar na samun nasara, amma bata-garin suna ta bullo da hanyoyin da za su kauce musu.

“Sun koma tare matafiya da masu babura suna zuke musu man fetur, suna shiga kauyuka neman nan fetur tare da tilasta wa mazauna su sayo a madadinsu.

“Abun damuwa a baya-bayan nan kuma shi ne sun fara mallakar wayoyin sadarwa na oba-oba,” amma jami’an tsaro na bibiya domin damko masu amfani da irin wadannan wayoyin.

Da yake jawabin ga taron ’yan jarida a Katsina ranar Alhamis, Sakataren Gwamnatin ya ce, daga watan Maris zuwa yanzu, an kama ’yan bindiga 724 a jihar.

Ya ce daga cikin ’yan bindigar da ake zargi an gurfanar da mutum 296 a gaban kotu, mutum 75 kuma ana kan gudanar da bincike a kansu.