✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun rufe Cibiyoyin kiwon lafiya 69 a Katsina

Galibi cibiyoyin kiwon lafiyar sun koma hannun 'yan ta'adda.

Akalla cibiyoyin kiwon lafiya 69 ne gwamnatin Jihar Katsina ta rufe a sakamakon matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a sassan jihar.

Dokta Shamsudeen Yahaya Kankia, Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko na jihar (SPHA) ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai ranar Talata a birnin na Dikko.

Dokta Yahaya ya bayyana cewa, wadansu daga cikin cibiyoyin lafiyar da lamarin ya shafa akwai guda biyu da ’yan bindiga suka kone su kurmus a Karamar Hukumar Batsari.

“Galibi cibiyoyin kiwon lafiyar sun koma hannun bata-gari, inda hatta firinjin sanyaya magunguna da aka samar a irin wadannan wuraren a yanzu ’yan bindigar ne ke amfani da su,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa, wasu daga cikin ma’aikatan cibiyoyin kiwon lafiyar da aka yi garkuwa da su kuma suka kubuta bayan biyan kudin fansa, na ci gaba da bayyana damuwa da korafe-korafen neman a sauya musu wuraren aiki.

Dangane da lalacewar wasu daga cikin cibiyoyin kiwon lafiyar a jihar, Dokta Kankia ya ce gwamnati a kammala duk wasu shirye-shirye na gyara cibiyar lafiya daya a kowacce daya daga cikin gundumomi 361 da ke fadin jihar.

Ya kuma bayyana kudirin gwamnatin jihar na ganin an gyara cibiyoyin lafiyar da ke jihar baki daya.