✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace almajirai a Sakkwato

Maharan sun kai farmakin ne da misalin ƙarfe 1:10 na dare wayewar garin yau Asabar.

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun sace almajirai 15 a wata Tsangaya a ƙauyen Gidan Bakuso da ke Karamar Hukumar Gada ta Jihar Sakkwato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan sun sace almajiran ne da misalin ƙarfe 1:10 na dare wayewar garin Asabar.

Shugaban makarantar, Liman Abubakar, ya ce kawo yanzu an nemi ɗalibai 15 an rasa, sai dai ya ce ba su tabbatar da adadin ɗaliban da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su ba.

Liman Abubakar ya kara da cewa, wannan ba shi ne karon farko da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen ba amma ba a taba sace dalibansu ba sai yanzu.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Gada- Gabas a majalisar dokokin jihar, Kabiru Dauda yayin da yake tabbatar da faruwar harin, ya ce ya samu kira daga ƙauyen da misalin ƙarfe biyu na dare cewa ’yan bindiga sun mamaye su.

“Na tuntubi mahukuntan kananan hukumomi da jami’an tsaro kuma na tabbata suna yin wani abu a kai.

Wakilinmu ya kuma samu labarin cewa, ’yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutum uku a ƙauyen Turba da ke Karamar Hukumar Isa, ciki har da dagacin kauyen.

Wani mamba mai wakiltar mazabar Isa, Habibu Modachi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yana kyautata zaton harin na ramuwar gayya ne bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki maboyar ‘yan bindigar kwanaki biyu da suka gabata.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma zai tuntubi jami’in ‘yan sandan shiyya na kananan hukumomin biyu.