✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa a kauyen Kaduna

Masu garkuwa sun sace Shugaban Cocin PFN a Jihar Kaduna

Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa ne sun sace Shugaban Cocin PFN a Jihar Kaduna, Apostle Emmanuel Egoh Bako da matarsa, Cindy Bako.

An dai sace su ne da yammacin ranar Juma’a a gidansu da ke Albarka a Fadan Kagoma, Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna tare da wani mai suna Douglas.

Fasto Emmanuel dai shi ne mamallakin Cocin Good News Power Base dake Kafanchan, kuma Sakataren Kungiyar Shugabannin Kiristoci ta Kudancin Kaduna (SKCLA).

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Joseph Hayab ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga ‘yan jarida ranar Asabar.

Ya bayyana faston a matsayin wani jigo a yankin, uba ga mutane da dama kuma ginshiki wajen samar da zaman lafiya a Kudancin Kaduna.

Daga nan sai Rabaran John ya yi kira ga jami’an tsaro su taimaka wajen ganin an ceto shi daga hannun masu garkuwar cikin gaggawa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin.

Ya ce tuni dakarunsu da aka girke a yankin suka dukufa da bincike don ganin sun ceto shi.