✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace gomman fasinjojin jirgin kasa a Edo

Kawo yanzu dai babu tabbas ko wani ya mutu a lamarin amma matafiyan da dama sun samu raunuka.

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji da dama a wata tashar jirgin kasa da ke karamar hukumar Igueben a Jihar Edo.

Wadanda abin ya rutsa da su dai na dakon shiga jirgin kasa ne zuwa Warri da ke Jihar Delta a lokacin da maharan suka far musu.

Kawo yanzu dai babu tabbas ko wani ya mutu a lamarin amma matafiyan da dama sun samu raunuka kamar yadda jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jami’in ya ce masu garkuwa da mutane dauke da bindigogi kirar AK 47, sun mamaye tashar jirgin ne da Yammacin ranar Asabar, inda suka rika harbi a iska kafin su yi awon gaba da matafiya da dama.

Harin na zuwa ne kasa da shekara guda bayan da ’yan ta’addan suka kaddamar da hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna inda suka kashe wasu fasinjojin jirgin tare da yin garkuwa da sama da 60 daga cikinsu.

Lamarin ya tilasta wa Gwamnatin Tarayya dakatar da sufurin jirgin kasa a hanyar Abuja zuwa Kaduna sama da watanni shida kafin maido da shi baya-bayan nan.