✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace kananan yara 20 a Neja

Masu garkuwa da yaran na neman Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa kuma suna azabtar da yaran

’Yan bindiga sun yi garkuwa da kananan yara 20 masu shekaru hudu zuwa 10 a garin Kusherki da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

16 daga cikin kananan yaran da ’yan ta’addan suka sace mata ne kuma a halin yanzu sun yi sayi uku a hannun masu garkuwa da su.

Mazauna garin sun ce masu garkuwa da yaran na neman Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa kuma suna azabtar da yaran.

Iyayen yaran sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki wajen kubutar da ’ya’yan nasu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa a ’yan makonnin nan ’yan bindiga sun dawo da cin karensu babu babbaka a yankunan Rafi da Magama da kuma hanyar Zungeru zuwa Tegina.

Hakan, a cewarsu ya jefa zullumi a zukatan wadanda suka fara girbe amfanin gonarsu.

Wani mazaunin yankin mai suna Abdullahi Ibrahim ya ce har yanzu akwai ’yan uwansu da aka yi garkuwa da wata hudu da suka gabata a hannun ’yan bindiga.