✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace sarki daga fadarsa a Taraba

Har cikin fardar sarkin da ke garin Pupule ’yan bindigar suka shiga suka yi awon gaba da shi da iyalan nasa

’Yan bindiga sun sace wani sarki mai daraja a biya tare da iyalansa da dogarinsa a Karamar Hukumar Yorro a Jihar Taraba.

Sarkin mai suna Alhaji Umaru Abubakar Nyala an dauke shi ne tare da matarsa mai juna biyu da dansa da dogarinsa da wasu talakawansa a daren Litinin.

Har cikin fardar sarkin da ke garin Pupule ’yan bindigar suka shiga suka yi awon gaba da shi da iyalan nasa, in ji majiyarmu a garin Pupule.

Majiyar ta ce ’yan bindigan fiye da 20 dauke da manyan makamai ne suka afka wa garin a tsakar daren Litini suna ta harbe-harbe, wanda ya sa jama’a tserewa daga garin.

Daga bisani ne maharan suka kutsa kai zuwa cikin fadar sarkin suna ruwan wuta.

Majiyar ta ce sai da gari ya waye aka gane cewa an sace sarkin garin da iyalansa da wasu mutane masu yawa a garin.

Wani mazaunin garin, Lawal mai doya, ya ce wannan shi ne karo na uku da ’yan bindiga suka kai garin suka sace mutane.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Taraba SP Usman Abdullahi ya tabbatar da aukuwar harin, amma ya ce har yanzu ba a ji duriyar sarkin da sauran mutanen ba.