✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako ’yar NYSC da suka sace a Zamfara

’Yan bindiga sun sako daya daga cikin masu yi wa kasa hidima bakwai da suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

’Yan bindiga sun sako daya daga cikin masu yi wa kasa hidima (NYSC) mata bakwai da suka yi garkuwa da su a Jihar Zamfara.

Hukumar Kula da Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta sanar da cewa ’yan bindigar sun sako ta ne tare da direban motar da suke ciki.

Idan ba a manta ba an yi garkuwa da masu yi wa kasar hidima ne a Jihar Zamfara a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin horas da su da ke Jihar Sakkwato.

Mai magana da yawun NYSC, Eddy Megwa, ya ce an sako ta ne a ranar Juma’a da taimakon  taimakon jami’an tsaro, inda ya bayyana cewa hukumar na da kwarin gwiwar jami’an tsaro za su yi duk abin da ya kamata wajen ganin suran ma an sako su.

Daga nan ya ce “ana shawartar masu yi wa kasa hidima da wadanda za su fara da su fifita tsaron rayuwarsu a kan komai; hakazalika hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da tsaro da kuma walwalarsu a kodayaushe.