✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sha da kyar a hanyar Kaduna-Abuja

Sojoji sun ragargaji masu garkuwa da mutane a hanyar Kaduna-Abuja

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce sojojin rundunar Operation Thunder Strike sun dakile harin masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A ranar Juma’a a dare ne gwamnatin jihar ta ce ta samu rahoton ’yan bindiga sun yi yunkurin kai hari a unguwar Kasarami da ke Karamar Hukumar Chikun da misalin karfe 7:38 na dare.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ya ce sojojin da ke sintiri sun yi artabu da bata-garin suka kuma fatattake su suka ranta a na kare.

“Yawancin ’yan bindigar sun tsere ne da raunukan harbi kuma sojoji na ci gaba da bin sawunsu, za mu yi wa jama’a karin bayanin halin da ake ciki nan gaba.

“Ragowar sojojin sun ci gaba da kula da hanyar domin kawar da cunkoson da aka samu sakamakon dauki ba dadin”, inji shi.

Da yake ba wa matafiya hakuri game da abin da ya faru, Aruwan ya ba su tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyinsu.

“Zuwa yanzu an bude hanyar komai na tafiya yadda ya kamata kuma sojoji na yin sintiri domin haka masu manyan laifi sakat”, inji shi.