’Yan bindiga sun tarwatsa masu bikin binne gawa, sun kone gidan mamaci | Aminiya

’Yan bindiga sun tarwatsa masu bikin binne gawa, sun kone gidan mamaci

‘yan bindiga
‘yan bindiga
    Titus Eleweke, Awka da Sani Ibrahim Paki

’Yan bindiga sun kai hari tare da tarwatsa wasu masu bikin binne gawa a garin Ezinifitte da ke Karamar Hukumar Nnewi ta Kudu a Jihar Anambra.

Lamarin dai ya jefa wanda suka halarci bikin cikin fargaba, inda suka rika guduwa domin neman tsira da rayukansu.

Daya daga cikin bakin da suka halarci bikin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa harin ya tilasta musu tashi ba niyya.

A cewarsa, “Lokacin da bayani ya iske ’yan bindigar cewa wani ya kawo jami’an tsaro cikin garin, sai suka shigo a wata mota kirar Sienna, sannan suka fara harbi ta ko ina.

“Mutumin da yake bikin binne wata ’yar uwarsa da jami’an tsaron tilas suka ranta a na kare, inda su kuma ’yan bindigar suka tsaya suka yi harbe-harbe tsawon lokaci, yayin da dukkan mutanen suka gudu, wasu ma suka fantsama cikin dazuka.

“Sun farfasa dukkan motocin da suke cikin gidan sannan suka gudu da wasu bayan sun sa wa gidan wuta, amma mun gode Allah mutane sun samu sun kashe wutar kafin ta yi barna sosai.

“Mutane da yawa da suka shiga cikin daji a can suka kwana, sai da safe suka fito. Ni kuma da wasu da muka shiga gidajen makwabta suka fito da mu suka ce ba wajenmu suka zo ba, ’yan siyasar da suka kawo jami’an tsaro suka zo farauta, da jami’an tsaron.

“In ka ga mutanen nan, suna dauke da muggan makamai, har na fara yanke kaunar kwanana ya kare, amma cikin ikon Allah, babu wanda aka kashe ko aka ji wa rauni,” a cewar ganau din.

To sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, ya shaida wa wakilinmu cewa ba shi da wata masaniya kan wani hari da aka kai Jihar.