✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji a Edo

Lamarin ya faru ne a kan titin Benin zuwa Auchi a jihar Edo.

Wasu ’yan bindiga sun tare wata mota kirar bas tare da yin garkuwa da mutanen da ke cikint.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:00 na safe a kan titin Benin zuwa Auchi a Jihar Edo a ranar Litinin.

An bayyana cewa ’yan bindigar sun tare wani bangare na titin da ya lalace inda suka yi wa motar kofar rago tare da kame fasinjojin da ke cikinta.

Bayan sun yi garkuwa da fasinjojin, sun dauke su zuwa cikin daji, wanda tun daga wannan lokaci ba a sake samun labarinsu ba.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Chidi Nwabuzor, ta wayarsa bai daga ba bare a ji ta bakinsa game da faruwar lamarin.