Daily Trust Aminiya - ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 19 a Neja

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 19 a Neja

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 19 a kauyen Kutunku da ke Karamar Hukumar Wushishi a Jihar Neja.

Wani ganau ya bayyana wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun far wa garin ne da safiyar ranar Litinin suna harbi ta ko’ina suna fatattar mutane.

Ya shaida ta waya ce maharan sun kuma lakada wa mazauna duka sannan suka yi awon gaba da maza 11 da mata takwas daga cikinsu.

A cewarsa, daga cikin matan da maharan suka tafi da su akwai wasu biyu da ake shirin daurin aurensu a karshen makon nan.

Sai dai ya ce har yanzu ’yan bindigar ba su tuntubi iyalan wadanda aka yi garkuwar da su ba.

Aminiya ta yi ta kokarin tuntubar kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja domin samun karin bayani, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba, har aka kammala wannan labarin.

Karin Labarai