✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 50 a Zamfara

Maharan sun kone rumbunan hatsi da gidaje a Karamar Hukumar Maru.

’Yan binidga sun yi awon gaba da mutum 50 a kauyen Tungar Baushe da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.

Yan bindigar sun far wa kauyen da ke yankin Mutunji ne bayan mazauna sun fara kwashe yakan abincinsu zuwa wani babban gari mai suna Rufan Tofa da ke makwabtaka da su.

Majiyarmu ta ce mutanen sun dauki matakin ne bayan yan bindiga sun kakaba musu haraji, kuma bisa alamu da gaske suke yi.

“Daga nan sai yan bindigar suka zo suka fara kona rumbunan hatsi da gidaje mutane.

“Sun tare mutanen garin da ke kokarin tserewa zuwa Ruwan Tofa.

“Mutanen da suka yi awon gaba da su daga Tungar Baushe sun kai kimanin 50 a lokacin harin.

“Daga mata da kananan yara babu wanda suka bari, duk kora su suka yi zuwa cikin jeji suka tafi da su.

“Yanzu kawai barnar da aka yi mana muke lissafawa, amma dai babu wanda aka kashe,” inji majiyar tamu.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin kakakin yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu kan lamarin, amma har muka kammala wannan rahoton hakar ba ta cimma ruwa ba.

Harin na zuwa ne washegarin ranar da aka sako dalibai mata 279 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar, a makarantar GGSS Jangebe da ke Karamar Hukumar Talata-Mafara.

Zamfara ta yi kaurin suna wurin ayyukan ’yan bindiga duk da matakan da Gwamnatin Jihar ta dauka da yin sulhu da su da kuma amfani da tubabbun cikinsu don jawo ra’ayin ragowar su ajiye makamansu.