✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga: Yadda bayan sulhu a Katsina da Zamfara mahara suka karkata jihohin Sakkwato da Neja

A lokacin da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya dauki salon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mohammad Bello Mutawalle wajen tattaunawa da yin sasanci da…

A lokacin da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya dauki salon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Mohammad Bello Mutawalle wajen tattaunawa da yin sasanci da mahara ko masu yin garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa a jiharsa, kuma aka fara samun saukin al’amarin, a hannu daya kuma rahotanni na nuna yadda maharan suka fara karkata zuwa wasu jihohin da ayyukansu na kama mutane da satar shanu da garkuwa da mutane da sauransu, musamman jihohin Sakkwato da Neja.

Kafin wannan sasanci na kwanan nan a Jihar Katsina, Karamar Hukumar Batsari ce ta fi dukan kananan hukumomi n jihar fuskantar hare-haren masu garkuwa da mutane da satar shanu da kisan kai ba gaira ba dalili da ake zargin Fulanin da ke cikin dajin ke yi. An yi zama na musamman a tsakanin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya da gwamnonin jihohin da suke fuskantar matsalar tsaron tare da shugabannin Fulanin da jagororin daba-daba na maharan, inda Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya karbi bakuncin taron a jiharsa. Gwamnan kuma shi ne Shugaban Kwamitin Tsaro da kuma Kwamitin Habaka Tattalin Arziki na Gwamnonin Arewa maso Yamma.

Al’amarin garkuwa da mutane da satar shanu da kashe-kashe ya kara ta’azzara, bayan wannan taro na Katsina domin babu ranar da ba a kai irin wannan hari a kananan hukumomin Jibiya, Danmusa, Safana, Kankara, Faskari, Dandume ko Sabuwa tare da Batsari wadda suka mayar tamkar za su share ta daga doron kasa.

Wannan  ne ya harzuka Gwamna Aminu Masari ya sake yin wani taro da wadansu shugabannin Fulanin, inda ya nuna bacin ransa kan saba alkawarin da suka yi, musamman yadda suka mayar da jihar wajen cin kasuwarsu. Har ya ce, “Babu dalilin da za a ce an yi sasanci na bai-daya amma a zo ana kai hari a wancan wajen amma an bar kaiwa a can. To lallai ne a tsayar da abin baki dayansa in kuma ba haka ba, to za mu yi amfani da karfin gwamnati. Domin ita wutar fetur in tana ci aka sanya mata ruwa ba ta mutu ba, sai a yi amfani da kemikal. To muna da kemikal din da za mu yi amfani da shi.”

Gwamna Aminu Masari ya shiga dazuka a makon jiya, inda ya fara daga yankin Dandume da Sabuwa. Ya je kauyen Dankolo, inda ya gana da shugabannin Fulani mahara na yankin. A lokacin da suke yi masa bayani kan irin kunci da matsin da suke fuskanta, wakillan Fulanin sun ce duk abubuwan da suke yi ba don suna so ba ne, tunda sun san zalunci ne. Sai dai sun ce akwai wadansu daga cikin jami’an tsaron da ke kara rura wutar rikicin. Sun ce, a yanzu haka akwai mutanensu da ke hannun su jami’an tsaro ba tare da an ce ga laifinsu ba balle a kai su kotu. “Irin wannan akwai su da yawa abin da ake yi mana. Bayan ba a kula da gina mana makaranta ko wajen shan magani da sauran kayan more rayuwa ba, alhali kuma har zabe mun yi, amma an bar mu haka nan,” kamar yadda wani daga cikin masu jawabin ya ce.

Bayan Gwamna Masari ya gama sauraren jawaban, sai ya ce yana so su sani cewa, wannan neman sasanci da ake yi ba wai gazawa ko tsoro ne ya sa gwamnati ta nemi a yi ba, a’a, ana son a samu zaman lafiya ne ta cikin ruwan sanyi. In sun bi, to a zauna lafiya, in kuma suka sake karya alkawari, to gwamnati za ta yi amfani da karfinta. Gwamnan har ila yau, ya yi alkawarin za a kawo musu mutanensu da ke hannun jami’an tsaro ba tare da an kai su kotu ba, su kuma za su sako wadanda suke garkuwa da su. Kazalika, gwamnati za ta duba matsalolinsu domin daukar matakin da ya dace.

A karshe ya ja hankalinsu cewa su ajiye makamansu ta hanyar mika su ga hukuma, wanda hakan zai tabbatar da dorewar zaman lafiya a tsakanin juna. “Bari ganin kana rike da bindiga, wata rana ita ce kuma za ta kashe ka. Yanzu ina Baharin Daji? Ba bindigar ce ta kashe shi ba? Saboda haka, ina jan hankalinku ku ajiye makamanku ku zo mu rungumi zaman lafiya. Kuma daga yau din nan ku je ku ci gaba da hidimominku a cikin sauran al’umma babu wanda zai kara taba ku, ku kuma kada ku taba kowa,” inji Gwamna Masari.

Wasu daga cikin yankunan da Gwamnan ya ziyarta domin sasanci da sulhu sun hada da Dansabau, Kankara, Faskari, Batsari, Jibiya da Dangeza a shiyyar Danmusa da Safana. Kuma ya je Jihar Maradi a Jamhuriyyar Nijar a ranar Asabar ta makon jiya bisa kudirinsa na ganin an kawo karshen wadannan hare-hare. Sai dai kafin ya tafi an fara ganin tasirin wannan zagaye da shiga kai-tsaye a cikin dazuzzukan da wadannan mahara suke. Tun daga ranar farko har zuwansa Maradi, ba a sake samun labarin kai wani hari ba.

Haka maharan sun sako mutaean da suka yi alkawarin sakowa a ranar Talatar da ta gabata, inda suka kawo wadansu mata 10 daga cikin mutum 20 ofishin Gwamna don tabbatarwa. Sannan duk inda aka gudanar da wannan taron sasanci, ana samun masu mika makamansu nan take.

Daga cikin nasarori da cika alkawuran da dukkan sassan biyu suka samu, akwai tsayar da kai hare-haren da musayar wadanda aka kama da mayar da makamai da sauransu.

A Jihar Sakkwato kuwa labarin ya canja, musamman inda aka yi zargin cewa wadansu daga cikin maharan da suka dade suna addabar jihohin Zamfara da Katsina, sun yi kaura zuwa Jihar Sakkwato, bayan sulhun da aka samu a wadancan jihohi.

Aminiya ta gano cewa a Jihar Sakkwato an kara samun yawan ’yan gudun hijira a kananan hukumomin Goronyo da Tureta da Rabah da Sabon Birni.

Maharan suna kai samamen dauki-daidai a garuruwan Gidan Sule da Dantayawa da Kuruwa da Kwarare a Karamar Hukumar Tureta, abin da ya kai ga mutanen kauyukan suka yi gudun hijira zuwa cikin garin Tureta, duk da cewa su ma mutanen garin ba su tsira ba, domin kwanan nan ne aka sace Magajin Gari da Magajin Rafin Tureta, sai da aka biya fansa aka sake su.

A Sabon Birini, maharan sun kai farmaki da maraicen Asabar da ta gabata a kauyen Katsira Tsanuna, suka kashe mutum shida, ciki har da mata uku, sai wadanda ke jinya a asibiti yanzu haka.

A Talatar da ta gabata ma sun shiga kauyen Gardin Ginge suka kashe wadansu tsofaffi uku, suka sace shanunsu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Muhammad Sadik ya tabbatar da kai farmakin, sai dai ya ce bai da labari kan harin da aka ce an kai a Karamar Hukumar Tureta har an yi garkuwa da dimbin jama’a a yankin, kuma gwamnatin jihar tana sulhu da maharan.

Dan Majalisar Dokokin Jihar mai wakiltar Karamar Hukumar Kebbe, Alhaji Isa Harisu ya bukaci Gwamnatin Jihar ta taimaka musu ta magance matsalar maharan da suka addabi yankinsu suna kashe mutane. Ya ce kwanan nan suka kashe wani mahaddacin Kur’ani da mutum shida, suka kona wasu a garin Kebbe, inda suka karbi kudin fansa daga mutanensu.

Da Aminiya ta tuntbu wani jami’in soja mai ritaya kuma mai sharhi kan lamurran tsaro a Najeriya, Aminu Bala Sakkwato ya ce akwai dalilai da ke kawo haka in aka lura cewa kafin Sakkwato Zamfara ce ta fi wannan matsalar da Katsina amma saboda matakin da aka dauka matsalar ta dawo nan.

“Bari in yi maka magana kan harkar tsaro a wannan gefe namu na Sakkwato, Zamfara da Katsina – suna saman wani daji ne da ya shiga har Nijar, ba komai a cikinsa in ba masu yin itace ba. Kan haka mutanen suka shiga cikinsa suna satar shanu daga baya suka hadu da masu satar mutane, sai dukansu suka bai wa satar mutane karfi don ta fi samar da kudi,” inji shi.

Ya ce “A hakikanin gaskiya abin ya yi kamari don Zamfara ta dauki mataki, akwai bambanci tsakanin maharan Sakkwato da na Zamfara, domin asalin rikicin Zamfara kafin ya rikide, fada ne tsakanin manoma da makiyaya, sai wadansu batagari suka shigo cikin lamarin Fulani suka karbe su, ganin yadda ’yan sa-kai Hausawa ba su raga wa mutanensu, suka aminta ana iya zuwa garin Hausawa a tayar da kowa a yi musu wulakanci. Abin ya yi zafi, kowa na kashe kowa in ya gan shi. Da Gwamnatin Zamfara ta shigo da maganar sulhu suka karba, bara-gurbinsu da suka mayar da abin sana’a  ne suka watsu a Katsina da Sakkwato. ’Yan ta’adda ne tsantsa suke kai hare-hare a Sakkwato kuma ba su da niyyar su bayar da kai, wannan shi ne ya rabo su da Zamfara,” inji Aminu Bala.

Ya ci gaba da cewa, “Har yanzu Gwamna Tambuwal bai ba harkar tsaro muhimmancin da ya kamata ba. An ce ana maganar sulhu da maharan, ba wata alama da ke nuna haka, domin har yanzu ba a nuna an san wadanda ke daukar makaman ba. Shin ’yan ta’adda ne ko mutanen gari da ake tsangwama? Matsalar da muke da ita a nan, gwamnati ba ta dauki lamarin da gaske ba. Da wuya mutanen su ba da makamansu, domin wadanda suka bayar da makamai a Zamfara ba ainihin ’yan ta’addan ba ne.

“Ni ban ga ana daukar matakin sulhu ba, ji kake yi an ce- an ce, gwamanati ta yi yarjejeniya da Fulani, ba mu sani ba da wa ake yi, su wane ne jagororin sulhun? Ba ya yiwuwa ka yi yarjejeniya ba ka fada wa mutane ba, domin suna son sanin inda aka dosa. Maganar sulhu da gwamnati ke fadi siyasa ce kawai kuma ya kamata a ajiye ta. Gwamna ya tsaya ya yi abin da shi ne hakkinsa na kare mutane da dukiyoyinsu.”

Ya shawarci gwamnatin cewa  ya kamata ta bai wa jami’an tsaro dama su fito da tsarin da za a bi domin magance lamarin, a nemo hakimai da shugabannin Fulani tunda mafi yawan maharan Fulani ne, a kuma samar da jami’an tsaron sirri na cikin gida.

“In aka yi haka, mutanen suka aminta da sulhu, a yi, in suka ki, a yake su. Gwamna ya yi amfani da kudin tsaron da ake ba shi ga jami’an tsaron domin magance matsalar. Ko bai yi aikin komai ba ya magance matsalar tsaro a Jihar Sakkwato, ya yi kokari. In dai har Zamfara na iya fahimtar matsalarsu su magance ta, babu wata hujja da Sakkwato za ta gaza,” inji shi.

Game da ’yan sandan jiha da wadansu ke ganin samar da su ne zai magance matsalar maharan, tsohon sojan ya ce “Akwai matsala ga samar da ’yan sandan jiha, ka dauki bindiga ka bai wa mutum ba ya da albashi, me kake zato in aka yi za a samu? Za a rika amfani da su wajen kuntata wa mutane, ana iya samun matsala da su jiha da jiha, bayan kuma ’yan siyasa za su rika amfani da su.”

Alhaji Muhammad Tambari Yabo, Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (mai ritaya), ya ce dole ne Jihar Sakkwato ta yi sulhu da maharan, in dai har Katsina da Zamfara za su yi. Yin sulhun ba dole sai mutane sun san ana yi ba, abu ne da ya shafi gwamnati.

“Abin ya yi kamari, akwai wasu abubuwa da ake yi bayan sulhu, ana kan yi kuma. Ma’ana ayyukan jami’an tsaro, duk duniya inda aka samu wannan tada kayar-baya ana sulhu. Sai dai ya kamata gwamanati ta shigo da masu ruwa-da-tsaki kan lamarin ta fahimtar da su kan bayanin gaskiya. Yana da matukar muhimmanci a shigo da kowa cikin lamarin domin kawo karshen lamarin da gundumawar kowa,” inji shi.

Ya ce maganar da wadansu ke yi kan samar da ’yan sandan jiha, zai magance matsalar rashin gamsuwa ce da ’yan sandan tarayya. Ya ce, “Ba ka hada wanda ya san gari ga dan gari da bako, a aiki kuma in aka kirkire su akwai kudin da za a kula da su, da samar musu kayan aiki, akwai jihar da ba a iya biyan albashi yaya za ka kirkiri abin da ba ka iya biya?”

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ce yanzu haka suna sulhu da maharan, domin ganin sun kawo karshen lamarin a jihar. Gwamnan ya fadi haka a ranar Talata da ta gabata, lokacin da ya karbi Mukaddashin Rundunar Soji ta Takwas, Birgediya Janar Aminu Bande wanda ya kawo masa gaisuwar ban girma.

A Jihar Neja kuwa, masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ne suka bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi hanzarin saka dokar-ta-baci dangane da tsaro a jihar.

Masanan sun gabatar da wannan bukata ce yayin wani taro da gwamnatin jihar ta shirya a ranar Talatar da ta gabata a Minna. Sun ce matukar gwamnati ba ta dauki wannan kwakkwaran mataki don magance matsalar tsaro a matakin kasa da jiha ba, Jihar Neja na iya zama tamkar yadda Zamfara ta zama a can baya game da matsalar tsaro.

Aminiya ta gano cewa ayyukan mahara da ke garkuwa da mutane da sace-sacen shanu da kashe-kashe sun sake bayyana a kananan hukumomin Shiroro da Rafi, inda aka rasa rayuka da dama kuma mutane sama da 1000 suka zama ’yan gudun hijira, bayan an tilasta su kaurace wa muhallansu.

Wakilinmu ya ce, jami’an gwamnati a jihar da kuma jami’an tsaro sun bayyana cewa babu shakka maharan da aka tarwatsa a jihohin Kaduna da Zamfara da Sakkwato suna rige-rigen zuwa jihar ta Neja, inda suke mamaye dajin Kamuku, wanda ya yi iyaka da jihohin.

Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja a nasa bangaren, ya  ce kashi mai girma na dukiyar jihar duk ana amfani da shi ne wajen magance barazanar tsaro. Ya ce sun kashe sama da Naira miliyan 470 zuwa yanzu, wajen magance matsalar.

Da take magana a yayin taron, tsohuwar Minista a Ma’aikatar Neja-Delta, Hajiya Zainab Kuchi ta bukaci gwamnatin jihar ta yi hanzarin daukar matakin dakile matsalar kafin “ta hallaka mu gaba daya.” Masana tsaron dai sun yi ittifakin cewa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta shiga cikin wannan tsari na sulhu da sasanci da gwamnatojin jihohi ke yi da maharan, ta yadda al’amarin zai zama na bai-daya, maimakon a rika magance wannan jiha, wata jihar kuma na fadawa cikin matsalar.