✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bingida: Matawalle zai tube sarakunan Zamfara

Ya haramta wa sarakai da shugabannin kanana hukumomi kwana a wasu wurare.

Gwaman Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle ya lashi takobin tube rawanin duk basaraken da ke kutungwila ga samar da tsaro a Jihar.

A zamansa da sarakuna, malaman addini da shugabanni tsaro, Matawalle ya umarci daukacin masu rikice da sarauta su rika kwana a yankunansu, kuma ya ce zai tube duk wanda ya saba umarnin.

“Daga yanzu an haramta wa sarakai kwana ba a yankunan da suke mulki ba.

“Dole ku zauna tare da jama’arku a koyaushe ku magance musu matsalar tsaro”, inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Shugabannin Kananan Hukumomi ma dole su zauna a matsayinsu na shugabannin tsaron kananan hukumomin nasu.

“An haramta musu kwana ba a cikin kananan hukumominsu ba face idan wani kwakwaran dalili na aiki ne ya sa hakan”.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa ta shafa wa idonta toka domin ta dandana wa masu hannu a matsalar tsaron jihar kudarsu.

“Masu hannu a matsalar tsaro ku kuka da kanku, za mu dau mataki kan rashin imanin da kuke nunawa da abin da ba ku zata ba”, inji shi

Matawalle ya ce Gwamnatin Zamfara na bin matsalar da lalama ne ne saboda sarkakiyar da ke tattare da tattaunawarta da ’yan bindiga.

Amma ya ce baragurbin ’yan siyasa na amfani da saukin kan gwamantin domin neman cimma munanan manufofinsu na siyasa.

A cewarsa hare-haren ’yan bindiga a baya-bayan nan hujja ce cewa miyagun ’yan siyasa na da hannu saboda yadda suka yi ta yada karairayi.

“Gwamnatin Jihar na iya kokarinta na tabbatar da doka da aminci a Zamfara amma wasu sun fi so su ji cewa an kai wa mutane hari.

“A kokarin bata-garin na nuna cewa gwamnatinmu ta gaza, babu abin da ya dame su da mutanen da ake ta kashewa”.

Ya ce bai damu ba don ya yi wa’adin mulki daya tak, muddin za a daina zubar da jinin mutane.

Gwamnan ya ce duk da haka Gwamnatin Zamfara a tsaye take domin gamawa tsagerancin miyagun mutane.