✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bola jari sun zargi ma’aikata da kone dukiyarsu ta N70m a Ogun

Sun zargi ma’aikatan na kokarin tilasta su don sun rika sayar masu da kayan jari bolar

Masu sana’ar bola jari a Jihar Ogun sun koka da abin da suka ce, wadansu ma’aikatan Ma’aikatar Kare Muhalli ta Jihar na yi na tsangwamarsu tare da tursasa su a kan sana’ar da suke neman abin dogaro da ita.

Sun ce ma’aikatan na kokarin tilasta su don sun rika sayar masu da kayan bola da suka tsinto a kan farashin da ma’aikatan suke bukata, wanda bai kai kashi daya cikin hudu na farashin da
kamfanoni suke saya a wajensu ba.

Malam Usman Muhammad Tambuwal, daya daga cikin shugabannin ’yan bola jarin wadanda suke harkokinsu a yankin Ogere a wata matattarar tara shara ta Gwamnatin Jihar Ogun shi ne ya shaida wa Aminiya hakan.

Ya ce a ranar Larabar da ta gabata, wata mace wacce jami’a ce da ke kula da motocin kwashe shara ta Gwamnatin Jihar Ogun ta zo inda suke adana kayayyakinsu wadanda suke kai wa kamfanonin su saya, ta zo ya sanya wa kayayyakin nasu wuta.

Ya ce ta zo ne tare da rakiyar jami’an tsaro a cikin motoci, wadanda suka hada da ’yan sanda da ’yan Amotekun.

“Sun kone mana daukacin kayayyakinmu da kudinsu ya haura Naira miliyan 70,
kamfanoni ne suke ba mu kudi mu rarraba wa yaranmu.

“Akwai kayayyakin da suke sayo wa a cikin gari, akwai kuma wadanda suke tsinta a bola, a nan muke tarawa nan kuma yaranmu suke da bukkokinsu inda suke kwana, kuma suke ajiyar kudinsu na sayen kayan.

A haka suka shigo mana a yammacin Larabar makon jiya suka ce yaran su fito daga saman bolar suka sanya mata wuta suka kone mana kayayyakin gaba daya,” inji Usman Tambuwal.

Daya daga cikin shugabannin ’yan bola jarin ya ce, matar da ta jagoranci kone masu dukiya ta dade tana addabarsu, inda a baya ta nemi sai dai su rika sayar mata da kayayyakin maimakon su kai wa kamfanonin.

“Kamfanin su ke ba mu kudi mu sayi kayayyakin mu kuma mu raba masu su saya, in mun tara mu kai wa kamfani su saya su cire kudinsu su ba mu riba, amma su ma’aikatan gwamnatin Jihar Ogun da ke kula da muhalli ba za su iya
ba mu kudin mu nemi kayan ba.

“Sannan ba za su iya sayen kayan da daraja ba, suna so mu sayar masu kilon da muke sayar wa Naira 100 a kan Naira 30, to, ai ba za a yi kasuwanci a haka ba, don haka muna neman Gwamnatin Jihar Ogun ta shiga tsakaninmu ta kuma bi mana haqqin dukiyarmu da suka kone,” inji shi.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce ’yan bola jarin daga sassan jihar suka yi dafifi a harabar ofishin gwamnatin jihar, inda suka nemi Gwamnan Jihar Ogun, Mista
Dapo Abiodun ya shiga tsakaninsu da ma’aikatan kula da muhalli na jihar.

Mai bai wa Gwamnan Shawara kan Harkar Tsaro, Olusola Zubair ne ya gana da ’yan bola jarin a lokacin da suka isa ofishin Gwamnan, kuma ya shaida wa
Aminiya cewa, ya saurari koken ’yan bola jarin, kuma zai isar da shi ga Gwamnan, “Na karvi lambobin wayar shugabanninsu, za mu neme su mu yi zama da su domin tattauna yadda za a bullo wa lamarin.” inji shi.

’Yan bola jarin da suka hadu a ofishin gwamnati da ke Oke Moson a Abeokuta, mazansu da matansu, sun shaida wa Aminiya cewa, a cikin kayan bolar suke
samun dan abin dogaro da suke kula da iyalansu, suka ce yau sama da wata uku ma’aikatan kare muhalli suna hana su yin sana’arsu.