✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi 8 sun shiga hannu a Kaduna

Rundunar ta ce su 'yan fashin na tare motocin daukar kayan abinci.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama ‘yan fashi takwas a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kakakin rundunar, Mansir Hassan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna.

Ya ce jami’an tsaron da ke sintiri a hanyar Kaduna zuwa Abuja ne suka kama su a ranar 27 ga watan Janairu.

“An yi nasarar cafke mutane takwas da ake zargin ‘yan fashi ne a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

“Sun tare masu ababen hawa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

“Suna tare ababen hawa da ke dauke da kayan abinci a kan hanyar.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Audu Ali, ya yaba wa jami’an da suka kama ‘yan fashin.

Kazalika, Kwamishinan ya jaddada aniyar rundunar na kawar da masu aikata laifuka a jihar.