✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi masu amfani da tsafin barci sun shiga hannu a Katsina

’Yan sanda sun cafke gungun wasu ’yan fashi da makami da ke amfani da tsafi su fasa gidaje a Karamar Hukumar Daura ta Jihar Katsina.

’Yan sanda sun cafke gungun wasu ’yan fashi da makami da suka kware wajen amfani da tsafi su fasa gidaje a Karamar Hukumar Daura ta Jihar Katsina.

Kakakin ’yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya ce ’yan fashin da dubunsu ta cika sun hada da wani mai shekara 50 da mai shekara 25 – daga Jigar Jigawa; na ukunsu kuma shekarunsa 23 kuma ya fito ne daga Kano.

Ya ce, dubun bata-garin ta cika ne bayan ’yan sanda sun samu bayanan sirri inda “Muka dakile su tare da cafke bayan sun kutsa cikin wasu gidaje biyar a Daura, sun yi awon gaba da kayan masu gidajen. 

“Wadanda ake zargin sun shaida wa ’yan sanda masu bincike cewa sun yi  amfani da layoyoyi ne sun sa masu gidaje barci har sai sun gama aikata barnar tasu.”

SP Gambo Isah ya ce, sun kuma amsa cewa sun samo layoyin ne daga wani boka a Jamhuriyar Nijar.  

Ya kara da cewa abubuwan da aka kwato daga wajensu sun hada da makullan da aka kirkira, kayan balla kofa; adduna; layukan waya guda biyar da kuma layoyi da sauransu.

Ya ce rundunar na ci gaba da gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya bayan sun kammala bincike.