✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun kashe mutum 6, sun sace kudade bayan fasa bankuna 4 a Edo

'Yan fashin sun fasa bankunan tare da dibar makudan kudade.

Akalla mutum shida ne suka rasa rayukansu yayin da gungun wasu ’yan fashi ya fasa bankuna hudu a yankin Uromi da ke Karamar Hukumar Esan ta Arewa Maso Gabas a Jihar Edo.

Rahotanni sun ce ’yan fashin sai da suka fara kai hari a caji ofis din ’yan sanda da ke yankin, kafin daga bisani su shiga bankunan.

Bakunan da ’yan fashin suka fasa sun hadar da bankin Zenith da na UBA da First Bank da kuma Union.

’Yan fashin, wanda kowanensu yake sanye da fuskar roba sun fasa kofar shiga bankunan, sannan suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

An kuma gano sun kwashi kudade masu tarin yawa daga cikin bankunan da suka fasa.

Wata majiya ta ce daga cikin wanda aka kashe har da jami’an ’yan sanda hudu, yayin karon-battar da aka yi.

Bayan tuntubar kakakin ’yan sandan Jihar, SP Bello Kontongs, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kontongs, ya tabbatar da fasa bankuna hudun da ’yan fashin suka yi, amma ya musanta cewar ’yan sanda hudu ne suka mutu.

Kakakin dai ya ce ’yan sanda biyu tare da wasu mutum hudu ne suka mutu baki daya a sakamakon harin.