✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun tare motar banki, sun daka wa kudin cikinta wawa

Harsasan harbe-harben dai sun yi wa biyu daga cikin motoci ukun da suke cikin ayarin kaca-kaca.

Akalla mutane biyu ne ake kyautata zaton sun mutu bayan ’yan fashi sun kai hari kan wata motar banki a jihar Ondo.

Rahotanni sun ce lamarin dai ya faru ne a kauyen Elemosho dake kan babbar hanyar Akure zuwa Ondo a Karamar Hukumar Ondo ta Gabas da yammacin ranar Alhamis.

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun isa wurin ne a wata mota kirar Lexus, suka yi wa motar bankin wacce ta yo dakon kudi kwanton bauna tare da wawushe kudaden da ba a san adadinsu ba daga cikinta.

Kazalika, an ce sun harbi mutum uku yayin musayar wutar da aka yi tsawon wasu ’yan mintuna, kafin daga bisani su tsere zuwa cikin daji.

“Daya daga cikin wadanda aka harba har yanzu yana nan da ransa, amma sauran biyun babu tabbacin ba su mutu ba,” inji wani ganau..

Mazauna garin suma sun rika fantsama cikin daji saboda tsira da rayuwarsu sakamakon karar harbe-harben da suka rika ji ba kakkautawa.

Harsasan harbe-harben dai sun yi wa biyu daga cikin motoci ukun da suke cikin ayarin kaca-kaca.

Daga bisani dai an gayyaci jami’an tsaron Amotekun wadanda suka garzaya da wadanda suka ji raunuka zuwa asibiti.

Kwamandan na Amotekun a jihar, Adetunji Adeleye ya tabbatar da faruwar lamarin, ko da yake ya ce ba a sami asarar rai ko daya ba.

Shima Kakakkin Rundunar ’Yan Sanda na jihar, Tee-Leo Ikoro ya ce ’yan fashin sun cika wandonsu da iska kafin zuwan jami’ansu.

Sai dai ya ce tuni suka dukufa da bincike domin bin sahunsu.