✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan gudun hijirar Afghanistan 6 sun mutu a hatsarin mota a Iran

Hatsarin ya faru ne a tsakiyar birnin Yazd na Iran ranar Litinin.

Akalla ’yan gudun hijirar Afghanistan shida ne suka mutu, wasu biyar kuma suka jikkata a wani taho-mu-gama da wata karamar mota ta yi da wata babbar mota a tsakiyar kasar Iran.

Hatsarin ya faru ne a kusa da wani shataletale da ke tsakiyar birnin Yazd ranar Litinin, kamar yadda Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasar Ahmed Dehghan, ya shaida wa kamfani  dillancin labarai na Mehr.

Ya ce daga cikin wadanda aka kashe din, har da wata mata, inda ya ce wadanda suka jikka kuma suna cikin tsaka mai wuya.

Sai dai babu wanda ya mutu a cikin babbar motar.

’Yan gudun hijirar Afghanistan da dama dai suna fama da yawan hatsarin mota a biranen Kerman da Yazd da ke Iran.

Su kan dai tafka gudu cikin sahara bayan tsallaka kan iyakar yankin Sistan-Baluchistan, don guje wa jami’an tsaro.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a shekarar 2020, akwai ’yan Afghanistan sama da miliyan 3.4 a Iran, ciki har da ’yan gudun hijira kusan miliyan biyu da kuma masu neman mafaka 800,000.