✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan gudun hijirar Afghanistan sun fara rokon a mayar da su gida

’Yan gudun hijirar sun ce hakurinsu ya fara karewa.

’Yan kasar Afghanistan da suka shiga kasar Burtaniya a kwanan nan bayan Taliban ta karbi mulki sun fara rokon a mayar da su gida saboda rashin tabbas a shirin tsugunar da su.

A karshen watan Agusta ne dai Firaminista Boris Johnson ya kaddamar da shirin da zai tallafa wa ’yan kasar da suka shigo Burtaniya domin su fara sabuwar rayuwa a kasar.

To sai dai matsalar karancin matsugunai ya sa dole aka ajiye ’yan gudun hijirar kimanin 7,000 a otal-otal.

Hakan ya sa wasu daga cikinsu suka ce sun fara gajiya.

Wani likita wanda yake aiki da ’yan gudun hijirar na tsawon makonni, amma bai amince a bayanai sunansa ba ya ce, “Na ji wasu daga cikinsu sun fara ce min suna son komawa gida.

“Wani mai shekara 67 daga cikinsu ya ce dole ne ya fita daga dakin otal din da yake, hakurinsa ya kare.”

Kazalika, shi ma wani dan kasar Afghanistan din wanda ya taba yin gudun hijira a shekara ta 2000, zamanin mulkin Taliban, ya shaida masa cewa, “Ni kawai abin da nake so shi ne ’yancin fita daga cikin otal din.”

Likitan ya ce da kyar ya lallashe shi tare da matarsa saboda yadda suka fusata.

Kazalika, akwai rashin tabbas kan kula da lafiyar mutanen da aka killace a otal din, inda wasu ke bayyana wargajewar shirin a matsayin gazawar gwamnati.

Ana dai zargin jami’an gwamnati da yin baki biyu, yayin da ayyukansu suke sabawa da abubuwan da suke fada.

A birnin Sheffield na Burtaniyar kuwa, ko a watan Agusta sai da wani yaro mai shekara biyar ya fado daga tagar dakin otal din da suke sannan ya mutu nan take.