✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan IPOB sun kai hari ofishin ’yan sanda a Akwa Ibom, sun kashe mutum 6

Maharan sun kuma sami nasarar lalata motocin rundunar da ma wasu muhimman kayayyaki a ofishin.

Rundunar ’yan sanda a jihar Akwa Ibom a ranar Asabar ta tabbatar da kai hari kan shalkwatar ofishinta dake Odoro Ikpe a Karamar Hukumar Ini ta jihar.

Ana dai zargin ’yan awaren Biyafara na IPOB ne suka kai harin, wanda ya yi sanadiyyar kashe mutum biyar da wata matar dan sanda.

Kakakin rundunar a jihar, SP Odiko Macdon ne ya tabbatar da hakan lokacin da yake duba irin barnar da aka yi sakamakon harin a ofishin.

Ya ce maharan sun kuma sami nasarar lalata motocin rundunar da ma wasu muhimman kayayyaki a ofishin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ofishin da ma wasu da dama a jihar ta Akwa Ibom sun fuskanci irin wadannan hare-haren, musamman da sanyin safiya a ’yan kwanakin nan.

Wani ganau a yankin ya ce maharan sun zo ne a motoci kirar Bas guda biyu da kuma wata kirar Sienna makare da mutane wadanda yawansu ya kai kusan 40, kowanne dauke da muggan makamai.

Ya ce da zuwansu kuma sai suka balle ofishin da misalin karfe 2:45 na dare, suka kashe jami’ai biyar dake bakin aiki, suka raunata wasu da dama sannan suka banka wa motocinsu wuta.

Shugaban Karamar Hukumar ta Ini, Mista Israel Idaisin shima ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ya jinjinawa matasan yankin wadanda ya ce sun ankarar da hukuma a kan lokaci, lamarin da a cewarsa ya taimaka matuka wajen rage yawan barnar tasu.

“Ina so mutane su kwantar da hankulansu, za mu zakulo tare da hukunta masu wannan aika-aikar nan ba da jimawa ba,” inji shi.