✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan Majalisar Osun sun kai ruwa rana kan rabon goron Kirsimeti

Buhun shinkafa da Naira 250,000 kawai kowannensu ya samu.

’Yan Majalisar Dokokin Jihar Osun sun murza gashin baki bayan da suka gano Gwamna Ademola Adeleke, ya ba su goron Kirsimeti har Naira miliyan 40 amma Shugaban Majalisar, Timothy Owoeye ya yi biris ba tare da ya ce musu uffan ba.

’Yan majalisar kimanin su 15, sun yi zargin Owoeye bai bayyana musu cewa Gwamnan ya yi musu kyautar kudi ba a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Osun Reporters ta rawaito ’yan majalisar na cewa, buhun shinkafa da kudi N250,000 kadai Shugaban Majalisar ya bai wa kowannensu a lokacin bikin.

Asirin ya tonu ne ta hannun wasu na kusa da Gwamna Adeleke bayan da suka dawo daga hutu, lamarin da aka ce ya yi matukar harzuka ’yan majalisar.

Majiyoyi sun nuna ’yan majalisar sun gano akwai wata boyayyar mu’amala tsakanin Owoeye da tsohon Gwamnan jihar, Gboyega Oyetola wanda ya kai ga yana rattaba wa tsohon gwamnan hannu kan neman bashi ba tare da saninsu ba.