✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya ne ke son in yi takara a 2023 —Atiku

Atiku ya ce ’yan Najeriya ne ke son ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce ’yan Najeriya ne ke son ya tsaya takarar shugaban kasa a babban zaben 2023.

Atiku ya sanar da haka ne ga manema labarai a Abuja, gabanin bayyana kudurinsa na neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

“Zan fito wannan takara ne don hada kan ’yan Najeriya,” inji shi a ranar Talata.

Atiku wanda ya sha fitowa takarar shugaban kasa, ya ce zai tsaya takara ne a 2023 domin kawo wa ’yan Najeriya sauki kan matsalolin da suke fuskanta.

Ya bayyana cewa ba shi da wata matsala a jam’iyyar PDP ko da sauran maso son fitowa takara, domin kuwa idan suka zauna za su fitar da dan takara cikin ruwan sanyi.

“Idan muka shiga daki muka zauna zamu fitar da dan takara babu wata matsala,” a cewar Atiku.

Da yake magana kan matsalar tsaro a Najeriya, Atiku ya ce rashin zaman lafiya da kasar ke ciki abun takaici ne da ke bukatar a tashi tsaye a magance.

“Babu shakka akwai matsalolin rashin zaman lafiya kuma wadannan abubuwan sun faru ne saboda rashin shugabanci na gari,” a cewar Atiku.

Ya kuma soki yadda gwamnati mai ci ta bari tattalin arzikin Najeriya ya samu tawaya, wanda hakan ya jefa miliyoyin mutane cikin kuncin rayuwa.