✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan PDP ’yan Arewa sun ziyarci Shugaban Jam’iyyar na Edo

’Yan Arewa sun amince da takarar Asue Ighodalo da Osarodion Ogie a zaɓen Gwamna da za a yi a ranar 21 ga Satumban 2024.

Ƙungiyar ’Yan Arewa mazauna Edo na Jam’iyyar PDP ta kai ziyarar ban-girma da taya murna ga Shugaban Jam’iyyar na Jihar, Dokta Anthony Aziegbemi wanda ya shaƙi iskar ’yanci sakamakon kuɓutar da shi da aka yi daga hannun masu garkuwa da mutane.

Ƙungiyar ta kai wa shugaban ziyarar ce a Sakatariyar Jama’iyyar da ke Benin babban birnin jihar a farkon makon nan inda ta gabatar da Sarahaisu Usman a matsayin Shugabar Riƙo na Jam’iyyar PDP na ’yan Arewa mazauna jihar.

A yayin ziyarar jagoran ’yan Arewa kuma shugaban ƙungiyar Alhaji Sahabi Aliyu Umaru, ya bayyana ƙudirin al’ummar Arewa na ganin Cif Ighodalo da Ogie sun zama Gwamnan Jihar da Mataimakinsa a zaɓen da ke tafe.

Ya ce ’yan Arewa mazauna jihar Edo sun amince da takarar Cif Asue Ighodalo da Osarodion Ogie a zaɓen Gwamna da za a yi a ranar 21 ga Satumban 2024.

Kuma suna ci gaba da shirye shiryen don ganin Jam’iyyar PDP ta samu nasara a zaɓen. Shugabar ya kuma ce, an naɗa Usman a matsayin

shugaban riƙo na Jam’iyyar PDP ’yan Arewa mazauna jihar, inda zai karɓi ragamar shugabanci daga hannun Malam Sani Muhammed wanda ya shafe shekara 16 a matsayin shugaban jam’iyyar ba tare da an zaɓe shi ba.

Cikin waɗanda suka yi jawabi a yayin ziyarar har da Alhaji Tijjani Aminu Muhammed shugaban ƙungiyar naƙasassu ’yan Arewa a jihar a inda ya tofa albarkacin bakinsa dangane da shugabancin Usman na ƙungiyar ’yan arewa na PDP.

A jawabin Cif Aziegbemi ya yaba wa al’ummar Arewa bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar, ya kuma tabbatar musu da cewa jam’iyyar za ta kira taron masu ruwa-da-tsaki nan ba da daɗewa ba don magance matsalar sauyi a shugabancin Jam’iyyar PDP ta Arewa baki ɗaya.