✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sa-kai sun kai wa rugagen Fulani hari a Sakkwato

’Yan sa-kai sun kai wa rugugen Fulani hari bayan ’yan bindiga sun kashe mutum uku sun sace wasu a Karamar Hukumar Binji ta Jihar Sakkwato

’Yan sa-kai sun kai harin daukar fansa kan wasu rugugen Fulani bayan ’yan bindiga sun kashe mutum uku tare da sace wasu da dama a kauyen Soro da ke Karamar Hukumar Binji ta Jihar Sakkwato.

Wani mazaunin kauyen Soro, ya ce, Da misalin karfe 1 na daren Litinin ne dandazon ’yan bindigar suka far wa kauyen “da garken dabbobin da sake zargin sun sato ne daga wasu kauyuka.

“A nan kauyen kuma sun kashe mutum uku, suka jikkata wasu uku sannan suka sace wasu da dama, cikin har da iyalan wani gida gaba dayansu.

“Bayan nan ne ’yan sa-kai da muke da su suka kai hari rugagen Fulani da ke kusa da mu suka kashe wasu mazaje daga cikinsu suka kona bukkokinsu.”

Shaidan namu ya ce, “akwai rade-radin cewa Fulanin sun yi wani taro kafin harin da aka kawo mana, mutanenmu na zargin a wannan zaman ne Fulanin suka shirya hari da aka kawo mana, saboda an jima ana zaman doya da manja tsakaninmu da su.”

Ya ce, “Yanzu haka wasu mutane sun tsere saboda tsoron harin daukar fansa,” amma wata majiyar ta ce kurar ta lafa bayan da aka tura jami’an tsaro yankin.

Kakakin ’yan sandan Jihar Sakkwato ASP Ahmad Rufa’i ya shaida wa Aminiya cewa, “’yan bindiga sun kai hari a kauyen Soro amma sojoji da ’yan sanda sun fatattake su.

“Duk da haka ’yan bindigar sun kona wasu gidaje, inda a sanadiyyar haka suka kashe mutum uku, wasu kuma suka samu raunuka.

“An kai harin daukar fansa amma jami’anmu sun shawo kan lamarin bayan zama da Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Kaigama ya yi da shugabannin kauyukan.

“Kwamishinan ya girke motocin sintiri guda hudu a yankin domin tabbatar da doka da zaman lafiya,” in ji jami’in.