✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda 4 sun mutu a hadarin mota a Delta

Mummunan hatsarin ya rutsa da wasu jami’an ’yan sanda a Asaba.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani mummunan hatsari ya rutsa da wasu jami’an ’yan sanda da ke cikin ayarin motocin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Najeriya, Farfesa Ibrahim Gambari da na Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola da kuma takwaransa na Ma’aikatar Kwadago da Samar da Aikin yi, Chris Ngige.
Hatsarin wanda ya auku a Yammacin Talata ya yi ajalin jami’an ’yan sanda hudu da ke cikin tawagar ayarin motocin manyan jami’an gwamnatin da ke ziyarar duba aikin wata gada a Asaba, babban birnin Jihar Delta.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, hadarin ya auku ne a yayin da wani dan sanda direba da ke tuka daya daga cikin motocin tawagar jami’an tsaron ta kwace, lamarin da ya kai ga fadawarta wani rami mai zurfi.
Wani ganau, John Okorie, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da wadanda lamarin ya rutsa dasu ke ja in ja kan kwanar da ta kai ga wajen aikin gina gadar Neja ta biyu a Asaba.
Sai dai da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya ce bai samu labarin faruwar lamarin ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.