✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto mutum 40, sun cafke mahara 10 a Taraba

Rundunar ta yi hadin gwiwa da mafarauta wajen samun nasarar ceto wadanda aka sace.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Taraba, David Iloyanomon, ya ce rundunar tare da hadin gwiwar mafarauta sun ceto mutum 40, sannan sun cafke ‘yan bindiga 10 a jihar.

Ya ce an ceto mutanen ne a wani kogon dutse da ke saman tsaunukan Yorro da ke Karamar Hukumar Zing a jihar.

Kwamishinan ’yan sandan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo, a ranar Litinin.

A cewarsa, sun cimma wannan nasarar ne sakamakon dabarun da suka yi amfani da su ta hanyar hadin gwiwa da mafarauta.

“Mun bullo da dabarar yin amfani da mafarauta da ’yan banga, wadanda suka fatattake su tare da ceto wadanda aka sace.

Ya kuma bayyana cewa sun yi nasarar cafke mahara 10 a lokacin da suke kokarin tserewa daga maboyarsu a saman dutsen.

Iloyanomon, ya ce sun mika wadanda suka ceto asibitin ‘yan sanda da ke Jalingo domin duba lafiyarsu.

“An yi garkuwa da da mutane a kauyukan Dilla, Lanko, da Gampu na Karamar Hukumar Yorro, da Dekko da Kotsensi na gundumar Monkin B a Karamar Hukumar Zing,” in ji shi.

“Maharan sun fasa idon mutum daya daga cikin wadanda aka ceto, sannan sun harbi wani wanda yanzu yana asibiti ana kula da lafiyarsa,” in ji shi.

Kwamishinan, ya ce ’yan sanda za su ci gaba da inganta hadin gwiwa da mafarauta da ‘yan banga a jihar don yaki da ta’addanci.