Daily Trust Aminiya - ’Yan sanda sun ceto uwa da ’yarta daga hannun masu garkuwa

Jami’an ‘Yan sanda

’Yan sanda sun ceto uwa da ’yarta daga hannun masu garkuwa

’Yan sanda a Jihar Adamawa sun samu nasarar tseratar da wata uwa da ’yar ta da masu garkuwa su kama.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da hakan ga wakilin mu bayan wadanda aka yi garkuwar da su sun kubuta.

An dai kama Hauwa Umara, tare da diyarta a ranar Asabar din da gabata a Unguwar Ngurore da ke Yola, babban birnin jihar.

An yi garkuwa da su ne har cikin gidan su da ke da makwabtaka da ofishin ’yan sandan Unguwar Ngurore, bayan da masu garkuwar su ka kai hari ofishin ’yan sandan.

Nguroje ya ce ’yan sandan da ’yan kato da gora ne suka far wa masu garkuwar a lokacin da su ke yunkurin yin awon gaba da wadanda suka kama.

Sai dai ya ce ba su yi nasarar kama ko daya daga cikin maharan ba, amma uwar-bari ta sa sun saki wadanda su ka yi yunkurin tserewa da su.

Bayanai sun ce a halin yanzu wadanda aka yi garkuwar da su sun samu nasarar komawa gida ba tare da wata matsala ba.

Karin Labarai