✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun hallaka dan bindiga yayin karbar kudin fansa

'Yan sandan sun yi artabu da maharan tare da kashe daya daga cikin su.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, ta hallaka wani dan bindiga yayin da yake hanyar zuwa karbar kudin fansa Naira miliyan uku a Karamar Hukumar Borgu a jihar.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ne, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ya ce sun kwato bindiga kirar AK-47 dan bindigar.

Abiodun, ya bayyana cewa wasu ’yan bindiga hudu, sun yi barazanar sace wani dan kasuwa a kauyen Bako-Mission da ke gundumar Pissa a Karamar Hukumar Borgu, idan ya gaza samar da Naira miliyan uku cikin kwana uku.

“Bayan samun bayanai, mun kai dauki inda muka yi artabu da su. Mun ceto wata matashiya mai shekara 22 da suka sace ba tare da ta ji rauni ba.

“Mun yi nasarar kashe daya daga cikin ’yan bindigar a lokacin artabun kuma mun kwato bindigarsa kirar AK-47. Sauran sun tsere da raunin harbin bindiga a jikinsu.

“Yanzu haka muna ci gaba da bincike don gano inda ragowar suka shiga. Za a ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”