✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun harbe mutum biyu har lahira

Wasu akalla mutum 10 sun samu raunin harbi a lokacin samamen.

’Yan sanda sun harbe mutum biyu har lahira tare da jikkata wasu da dama a garin Ajaawa na Karamar Hukumar Ogo Oluwa ta Jihar Oyo.

Shugaban Karamar Hukumar, Seun Ojo, ya ce baya ga mutum biyun da suka bakunci lahira, akwai sama da 10 da suka samu raunin harbi bindiga a lokacin wata mamaya da ’yan sanda suka kai a yankin a tsakar daren Talata.

Ya ce ’yan sandan da suka shigo yankin daga Ofishin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, sun dauki tsawon lokaci suna luguden wuta a tsakar daren.

A don haka, ya yi kira tare da basaraken yankin — Alajaawa na Ajaawa, Oba Thompson — ga Sufeto Janar din da ya kawo musu dauki kan abin da suka kira hare-haren jami’an ’yan sanda a yankin.

Da suke jawabi ga ’yan jarida a garin Ibadan, shugabannin biyu sun yi zargin wani babban mutum ne a yankin ya hada baki domin tayar da fitinar ta hanyar amfani da ’yan sanda.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin haske kan lamarin daga mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Oyo, Adewale Osifeso, amma ya yi masa alkawarin yin hakan idan ya samu bayanai.