✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kama wanda ya kashe mahaifinsa

‘Yan sanda da taimakon ‘yan banga sun kama wani matashi, Chisom Ogum, da ya kashe mahaifinsa mai shekara 70 tare da binne shi cikin sirri…

‘Yan sanda da taimakon ‘yan banga sun kama wani matashi, Chisom Ogum, da ya kashe mahaifinsa mai shekara 70 tare da binne shi cikin sirri a kauyen Umuomaku, na karamar hukumar Orumba da ke jihar Anambra.

A cewar rahotanni, matashin da ba a san abinda ya harzuka shi ba, ya yi amfani da shebur wajen kashe mahaifin nasa sa’annan ya tona rami ya binne shi.
Wata majiyarmu ta ce, matashin ya yi kokarin tserewa amma mutanen gari suka kama shi suka yi masa dukan kawo wuka, sa’annan suka sanya shi ya tono gawar mahaifin nasa daga inda ya binne ta.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya ce lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Agustar 2020.
Ya kuma ce jami’ansu masu fararen kaya sun ziyarci inda abun ya faru tare da daukar hotunan gawar kafin daga bisani su kai ta dakin ajiye gawawwaki na asibitin Umunze, domin a tabbatar da dalilin mutuwarsa in har likita ya ce ya mutu.
Ya kuma ce sun gano sheburin da ya yi amfani da shi wajen kashe mahaifin nasa.
Kakakin ya ce tuni kwamishinan ‘Yan sandan jihar, John B. Abang, ya umarci a mayar da shi sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin ci gaba da bincike.