✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘’Yan sanda sun kashe min da akan cin hancin N100’

Wata mata da mijinta ya rasu, Misis Mfon Udoidiong ta zargi jami’an ’yan sanda da kashe mata danta shekaru hudu da suka gabata saboda N100.

Wata mata da mijinta ya rasu, Misis Mfon Udoidiong ta zargi jami’an ’yan sanda da kashe mata danta shekaru hudu da suka gabata saboda ya ki ba su cin hancin N100.

Matar, wacce take zama a garin Nkek, dake Karamar Hukumar Ukanafun a jihar Akwa Ibom ta yi zargin ne lokacin da take bayar da ba’asi a gaban Kwamitin Bin Diddigin Zargin Cin Zalin ’Yan Sanda a Uyo babban birnin jihar ranar Alhamis.

Mfon, wacce karamar ’yar kasuwa ce, ta ce dan nata, marigayi Imo Udoidiong  ya gamu da ajalinsa ne a wani gidan kallo, jim kadan da dawowarsa daga makaranta.

A cewarta, bayan wasu ’yan sa’o’i sai wani abokin dan nata ya zo yake shaida mata cewa wani jami’in dan sanda ya bindige shi har lahira bayan ya bukaci kudi daga hannunsa.

Ta kara da cewa iyalan dan sandan sun bata N200,000 domin sayen likkafani su binne shi, amma tun daga nan suka yi watsi da su.

“Iyalan dan sandan sun yi alkawarin bani Naira miliyan daya saboda in samu na ci gaba da rayuwa ta, amma har yau babu wanda ya bamu ko sisin kwabo. N200,000 kwai suka bani domin sayen likkafanin binned an nawa,” inji matar.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idanunsa Ubong Monday ya shaidawa kwamitin cewa mamacin, wanda ajinsu daya da shi a makarantar sakandire ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ya je sayen wasu kayan jikin babur.

Ubong ya kuma ce sai da mamacin ya roke shi da ya rage masa hanya saboda shi a kan babur yake.

Daga nan ne kuma lauyan mamacin Mista Augustine Udoh ya bukaci kwamitin da ya tabbatar an kori jami’in da ake zargi daga aiki tare da gurfanar da shi a gaban kuliya don ya girbi abinda ya shuka.

Kwamitin, wanda ke karkashin shugabancin Mai Shari’a Ifiok Ukana (mai ritaya) ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 21 ga watan Janairun 2021.