✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 10 a Neja

’Yan sanda biyu sun kwanta dama yayin musayar wuta da ’yan bindigar.

’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga 10 suka kuma dakile harin bata-garin a Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Wasu jami’an ’yan sanda biyu kuma sun rasu a dauki-ba-dadin da suka yi da ’yan bindigar a kauyen Kundu a ranar Lahadi.

Mazauna kauyen ne suka tabbatar da hakan a lokacin ziyarar da gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello ya kai yankin, inda suka ce ’yan sandan sun yi nasarar fatattakar ’yan  bindigar da suka yi yunkurin kutsawa garin.

Gwamnan ya ziyarci yankin ne domin jajanta wa mutanen garin da kuma jinjina wa ’yan sandan bisa namijin kokarin da suka yi.

“Na yaba da kokarinku ina kuma ba ku tabbacin samun cikakken goyon bayana da duk abubuwan da kuke bukata na gudanar da ayyukanku cikin nasara.

“Saboda haka nake so su saki jiki ku bayyana bukatunku, ni kuma zan yi duk mai yiwuwa wajen biya muku su,” inji shi.

Ya ce gwamnatinsa ta yi tanadi domin samar da kayan aiki ga jami’an tsaro kuma nan gaba kadan kayan za su isa Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar.

Gwamnan ya kai ziyarar ce tare da Kwamandan Rundunar Sojin Jihar, Birgediya Ademola Adedoja da kuma Kwamishinan ’Yan Sanda, Adamu Usman.