✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun kubutar da dan shekara 46 daga hannun ‘yan bindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara sun yi nasarar ceto wani mutum mai suna Alhaji Musa Atere da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi ranar…

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara sun yi nasarar ceto wani mutum mai suna Alhaji Musa Atere da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi ranar Talata.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da ceto mutumin a kauyen Oko Olowo da ke garin Ilorin a ranar Laraba.

“An yi garkuwa da Atere a ranar Talata da misalin karfe 6 na safe a kan titin Ogundele/Madi, yayin da yake kokarin kai diyarsa asibiti a nan Kwara.

“Yana tare da matarsa a cikin motar yayin da suka yi awon gaba da shi tare da kwace wasu kudade da ke jakar matar tasa,” in ji Okasanmi.

“Da farko masu garkuwar sun nemi cewa sai an basu Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansarsa, kafin su sake shi.”

“Mun samu nasarar ceto Atere ne bayan tattara bayanan sirri sannan muka yi wa maboyar wanda suka yi garkuwa da shi dirar mikiya.”

“Bayan mun zagaye dajin, sai ‘yan bindigar suka ankara, lamarin da ya sanya suka tsere suka bar Atere a inda suka daure shi.”

A cewar Mista Ajayi, bayan tserewarsu, shi ma Atere ya ranta a na kare zuwa wani kauye da ke kusa dajin, inda a nan ne mutanen kauyen suka kawo shi babbar hanyar Oko Olowo.