✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwato bindigogi da shanu 200 a Zamfara

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wasu mutum hudu bisa zargin  kashe wasni Bafulatani makiyayi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abutu Yaro, yayin gabatar da…

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta kama wasu mutum hudu bisa zargin  kashe wasni Bafulatani makiyayi

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Abutu Yaro, yayin gabatar da su a ranar Lahadi ya ce jami’an Rundunar sun kuma kwato shanu 200 daga masu satar dabbobi.

“Mun kwato shanu 200 bindigogi kirar AK-47 guda biyar, motoci uku da harsasai masu tarin yawa,” inji shi.

Kwamishinan ’Yan Sandan Ya ce shirin samar da aminci da gwamnatin jihar ke jagoranta a jihar ya yi gagarumar nasara.

Daga cikin nasarar, a cewarsa, ’yan bindiga sun mika wa gwamnatin bindigogi kirar AK-47 guda uku da harsasai 47

Ya jaddada aniyar rundunar na ci gaba da tattaunawa masu ruwa da tsaki domin samun nasara a yaki da ayyukan ta’addanci.

“Za mu ci gaba da shirinmu na samar da zaman lafiya da kuma tuntubar dukkannin masu ruwa da tsaki domin kawo karshen dukkannin ayyukan ’yan bindiga,” inji shi.