✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Kogi

Sun kwato bindigogi da harsasai daga hannun masu garkuwar

’Yan sanda a Ajaokuta, Jihar Kogi, sun kubutar da wasu mutane daga hannun ’yan bindiga tare da kwato bindigogi kirar AK47 guda biyu da kuma harsasai daga masu garkuwar.

Ofishin ’yan sanda na Ajaokuta ya ce a ranar Lahadi da rana ne wasu mutane hudu suka yi garkuwa da wani mutum a daidai shataletalen PYN da ke garin zuwa cikin daji.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar, DSP Williams Ayah, ya ce na ntake ofishin ya tura jami’ai karkashin jagorancin CSP Shola Night, su bi sawun masu garkuwar a cikin dajin inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar.

Ya ce bayan dauki ba dadin ne ’yan sandan sun yi nasarar kubutar da mutanen da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, Ede Ayuba Ekpeji, ya bukaci mutanen Jihar da su sanya idanu da mika rahoton duk wani motsi da ba su natsu da shi ba ga jami’an ’yan sanda.

Ya kuma roke su da su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi ga ofishin ’yan sanda ko wata hukumar tsaro tsaro mafi kusa don a samu a cafke shi.