✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun nemi Murja Kunya ta biya su diyyar Naira dubu 500

Mai Shari’a Nasiru Saminu ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga Maris domin yanke hukunci.

Rundunar ’yan sandan Kano ta nemi fitacciyar jarumar nan ta TikTok, Murja Ibrahim Kunya da ta biya ta diyyar Naira dubu ɗari biyar.

Rundunar ’yan sandan ta shigar da wannan buƙatar ce a gaban Babbar Kotun Jihar Kano da ke titin Miller karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasiru Saminu.

Rundunar ta ce neman diyyar ya biyo bayan shigar da su kara da jarumar TikTok ɗin ta yi ba tare da sun aikata laifin komai ba sai dai kawai don bata wa shari’a lokaci.

A martanin da ta mayar a gaban kotun, rundunar ta bakin lauyanta Barista Abdussalam Saleh Danmaidaki, ta nemi kotun da ta cire sunanta daga jerin waɗanda ake kara saboda ba su da masaniya kan shari’ar.

“Mu da ake kara a wannan shari’ar ba mu da masaniya a kan abin da ya shafi bangarorin biyu, kasancewar ba a kawo mana ƙorafin da zai sa mu gayyaci kowa ba. Saboda haka duk abin da aka kawo wa kotu babu gaskiya ko ɗaya a ciki.”

Ana iya tuna cewa a makonnin da suka gabata ne Murja ta shigar da ƙara gaban kotun tana kalubalantar Antoni-Janar na Kano, da Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, Uta Ahmad, da Kwamishinan ’Yan sandan Kano, da Hukumar Hisbah, da Hukumar da ke kula da Asibitocin Kano, haɗi da Asibitin Kula da Masu lalurar kwakwalwa da ke Dawanau.

Da yake mayar da martani, Lauyan Gwamnatin da ke wakiltar waɗanda ake kara daga na daya zuwa shida, Barista Salisu M. Tahir, ya bayyana cewa Hukumar Hisbah tana da hurumi a kan duk wani abu da ya shafi rashin da’a a cikin al’umma, la’akari da sashe na 10 na dokar da ta kafa hukumar a shekarar 2000.

A cewarsa, ainihin abin da ya faru shi ne wacce take ƙara ta aikata abubuwa na rashin tarbiya wanda ya saba da dokar da ta kafa Hukumar Hisbah da Addinin Musulunci, da kuma al’adun al’ummar Jihar Kano.

Ya bayyana cewa dangane da hakan ne Hukumar Hisbar karkashin sashe na 10 na dokokinta ta gayyaci Murjar domin yi mata wa’azi.

“Daga nan ne kuma ta kamo ta [Murja] sannan ta damka ta ga Hukumar da ta dace.”

Haka kuma, Lauyan ya ce Gwamnati da Hukumar da ke kula da Asibitocin Jihar Kano ba ta taba hana ’yan uwan Murja ko lauyoyinta damar ganinta ba, illa iyaka an sanar da su cewa sai dai su zo lokacin da aka kebance domin ziyarar marasa lafiya.

Aminiya ta rawaito cewa, tun da fari lauyoyin mai ƙara karkashin jagorancin Barista Umar Faruk Aliyu na neman kotun ta saurare ta, sannan ta biya musu dukkanin bukatun da suka nema.

“Babbar bukatarmu ita ce kotu ta umarci Asibitin Kwararru na Muhammad Abdullahi Wase da ya dawo wa wacce muke tsaya wa wayoyinta na salula kirar IPhone da kuma katin kuɗi na Bankin Zenith.”

Bayan sauraron duk bangarorin, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga Maris domin yanke hukunci.