✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda 14,809 za su fuskanci hukunci

Akalla mutum 14,809 da ake zargi da tayar da kayar baya ne za a gurfanar da su gaban kuliya bisa laifin ta’addanci da sauran miyagun…

Akalla mutum 14,809 da ake zargi da tayar da kayar baya ne za a gurfanar da su gaban kuliya bisa laifin ta’addanci da sauran miyagun ayyuka a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kwamandan runduanr Operation Hadin Kai, Manjo-Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa mutane 70,593 da suka hada da ’yan Boko Haram da ’yan ta’addar ISWAP da iyalansu sun mika wuya ga sojoji.

Ya ce daga cikin wadanda suka mika wuya, sama da 14,800 da ake zargin ’yan ta’adda ne, 20,955 kuma mata ne sai yara 35,209.

Kwamandan ya ce an wanke mutumn da aka tsare a hannun rundunar hadin gwiwar da kuma ofishin babban mai shari’a na tarayya.

Ya ce: “Mun fara nazarin shari’o’in mutanen da ake tsare da su a cibiyar binciken hadin gwiwa.

“An mika wadanda ake zargin ga Gwamnatin Jihar Borno da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).

Ya ci gaba da cewa: “A ranar 13 ga Yuli, 2022, an kama Haruna Fulani da Usman, wadanda ake zargi da kai wa kwamandan dabaru Adamu Ngulde hari a tsaunin Mandara a karamar hukumar Gwoza.”

Ya ce tun da aka fara aikin Operation Desert Sanity, ’yan ta’addan sun karaya ta yadda ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da cin nasara ba.

Ya ci gaba da cewa. ‘yan ta’addan sun fi neman abinci da kayan aiki, kuma a sakamakon sojoji sun “kawar da ’yan ta’adda da dama a lokacin da aka share ayyukan sharar fage na baya-bayan nan.”