✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan ta’adda 15 sun shiga hannu a Legas

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Legas ta sanar da cafke wasu mutum 15 da ake zargin su da aikata laifuka da suka danganci na…

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Legas ta sanar da cafke wasu mutum 15 da ake zargin su da aikata laifuka da suka danganci na kungiyoyin asiri da ta’addanci.

Haka kuma ta sanar da cewa ta samu nasarar kwato wasu muggan makamai a hannun gungun mutanen da ke addabar mazauna yankunan Lekki da Ajah a birnin na Iko.

Mai magana da yawun Rundunar, Muyiwa Adejobi cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce an cafke mutanen ne kafin su farga wajen kai wani hari da suka kitsa.

Ya ce da misalin karfe 4 na safiyar Litinin ne yayin wani aikin kai agaji, jami’an rundunar suka cafke wani matashi dan shekara 20, rike da karamar bindiga kirar gida a yankin Agunfoye.

Adejobi ya ce bayan kama matashin ne aka tsananta bincike kuma aka samu nasarar cafke wasu mutum 13 da ake zargi mambobin wata kungiyar asiri ce mai sunan Aiye Confraternity.

Ya kara da cewa a ranar ce kuma jami’an ’yan sanda na sashen Akodo suka cafke wani dan kungiyar asiri mai shekara 20, yana shirin yin fashi da a wani gida da ke unguwar Ibeji a yankin Lekki.