✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta haramta wa Gwamnatin Kano yin rusau

Mai shari’a Simon Amobeda, ya bayyana cewa gine-ginen an mallake su be bisa ka’ida, don haka ba za a iya rushe su ba sai da…

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta hana gwamnatin jihar ci gaba da rusa gine-ginen da ke unguwar Salanta wanda tun farko ta sanya musu alama.

A yayin da yake yanke hukunci, Mai shari’a Simon Amobeda, ya bayyana cewa gine-ginen an mallake su be bisa ka’ida, don haka ba za a iya rushe su ba tare da amincewar masu su ba.

Masu shigar da kara sun garzaya kotu ne a watan Yulin 2023, suna neman ta kare musu hakkinsu na kadarorin da suka mallaka, amma gwamnatin jihar ta sanya musu alamar rugujewa.

A lokacin ne kotun ta ba da umarnin wucin gadi da ke hana gwamnatin jihar daukar mataki har sai an yanke hukuncin karshe.

Wadanda suka shigar da karar sun hada da Alhaji Ali Mai kusa da Ali Rabiu Awwalu da Balarabe Sani Salanta da Umar Ibrahim Batayya da Salisu Idris Daneji da Alhaji Ibrahim Sadi da Umar Shittu Sharubutu.
Lauyan masu kara Kabiru Ishaq Kofa ya ce bisa ga hukuncin da kotun ta yanke, “Gwamnatin Kano ko hukumar raya birane ta jihar (KANUPDA), ko wakilansu, har abada an hana su hari ko rushewa ko ma kwace gine-ginenba tare da amincewar masu su ba”.

Lauyan ya ce wadanda yake karewa sun bi duk matakan shari’a kafin su mallaki kadarorin tun kafin zuwan wannan gwamnati.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin rusa wasu gine-gine da ake zargin mallakarsu ba bisa ka’ida ba ne kwanaki kadan bayan hawansa mulki.

Gwamnan ya zargi gwamnatin da ta gabata da bayar da filaye ga wasu ’yan baranda da kuma sayar da wasu filaye na makarantun gwamnati da makabartu da masallatai ba tare da bin ka’ida ba.

Lauyan wadanda ake kara ZB Sawi bai yi tsokaci ba kan hukuncin.

Kokarin jin ta bakin babban lauyan jihar kuma kwamishinan shari’a Haruna Isa Dederi kan hukuncin da kuma matakin da gwamnati za ta dauka na gaba bai yi nasara ba.